HAMADA FM - Radio Station

Gwamnatin Nijeriya ta amince da dage aikin kidayar shekarar 2023 na kidaya adadin mutane da gidaje da aka shirya fara yi a ranar 3 ga watan Mayun wannan shekara.

 

Hakan na zuwa ne bayan wata ganawa da shugaban Kasar, Muhammadu Buhari, ya yi da wasu mambobin majalisar zartaswar kasa, da shugaban hukumar kidaya ta kasa a fadar shugaban kasa a ranar Juma’a.

 

Yayin zaman, hukumomin sun jaddada bukatar da ke akwai na yin kidayar jama’a da gidaje tun bayan wadda aka yi shekara 17 da suka gabata domin tattara bayanai da za a yi amfani da su wajen fitar da tsare-tsaren da za su taimaka wa ci gaban kasa.

 

Cikin wata sanarwa da ministan yada labarai da raya Al’adu, Lai Mohammed ya fitar a ranar Asabar, Shugaba Buhari ya yaba da irin tsare-tsaren da aka yi domin gudanar da kidayar ta 2023.

 

Kazalika, ya jinjina wa hukumar bisa fito da tsare-tsare masu inganci da zasu bayar da dama a gudanar da hakikanin kidaya.

April 29, 2023

Written by:

1 Comment

  • mustapha isah

    13/01/2023

    nice

Comments are closed.