HAMADA FM - Radio Station

 

Majalisar dinkin duniya ta nuna damuwa gameda yadda ake samun cigaba da fashe-fashen gidajen yari a Kasar Sudan, lamarin da yayi sanadiyar tserewar manyan masu laifin yaki daga gidajen yarin.

Kakakin Majalisar, Ravina Shamdasani, ta bayyana wa manema labarai a birnin Geneva, cewa kungiyar ta shiga damuwa saboda tserewar wadannan fursunonin, duba da cewa hakan ka iya rura wutar rikicin da ake kokarin kashewa a halin yanzu.

Kalaman nata na zuwa ne bayan da aka samu gidajen yari da dama da aka fasa cikinsu har da babban gidan kason da aka tsaren manyan masu laifin yaki.

 

Sai dai, Majalisar Dinkin Duniyar ta ja hankali da cewa rikicin na Sudan na kara rura rikicin kabilanci a yankin yammacin birnin Darfur wanda yayi sanadiyar asarar rayuka kusan 100 cikin ‘yan kwanaki.

April 29, 2023

Written by: