HAMADA FM - Radio Station

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya tsawaita wa’adin aikin mukaddashin kwanturola janar na hukumar kula da shige da fice ta kasar, Isah Jere Idris, har zuwa ranar 29 ga watan Mayun, 2023.

 

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaba Buhari ya fitar dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan sa, Farfesa Ibrahim Gambari.

 

Wannan shine karo na biyu da aka tsawaita wa’adin aikin Jere bayan cikar shekarun ajiye aikin sa.

 

A nasa bangaren, mai Magana da yawun hukumar kula da shige da fice ta kasa, Tony Akuneme, ya tabbatar da wa manema labarai cewa shugaban hukumar ya samu wasikar dage lokacin yin murabus dinsa har zuwa karshen wa’adin gwamnati mai ci.

April 29, 2023

Written by: