Rundunar ’Yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama bindigogi kirar AK-47 guda hudu da aka yi kokarin yin fasakwaurinsu zuwa Jihar Kano.
Cikin wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya fitar ya ce a ranar Juma’a ne ’yan sanda da ke sintiri a Kwanar Garko da ke kan hanyar Bauchi zuwa Kano suka gano bindigogin a cikin wata bas kirar Hiace.
Abdullahi Kiyawa, ya ce Masu motar na hango ’yan sanda, sai motar ta fara kokarin juyawa, inda daya daga cikin mutanen motar ya fito ya jefar da kunshin wani abu a cikin buhu, suka ja motar suka tsere.
Daga baya da ’yan sanda suka duba sai suka gano bindigogi kirar AK-47 guda hudu a ciki.
Sanarwar ta ce rundunar tana ci gaba da bincike domin kamo mutanen da suka tsere